Da Alamu Kungiyar Taliban da Gwamnatin Afghanistan Zasu Kpma Teburin Shawara

Shugaba Ashraf Ghani na Afghanistan yana shan hannu da Firayim Ministan Pakistan Nawaz Sharif

Jiya Laraba wasu jami'an kasar Pakistan sun fada cewa kungiyar Taliban da gwamnatin Afghanistan zau koma teburin shawara makon gobe

Ana sa ran za'a koma teburin sulhu tsakanin kungiyar Taliban da gwamnatin Afghanistan watakil makon gobe, kamar yadda aka ji daga wasu jami'an kasar Pakistan jiya Laraba.

Jami'an suka kara da cewa, suna son ganin an wakilci hukumomin kasa-da kasa atsawon shawarwarin, saboda sanin akwai tarihi na rashin yarda tsakanin Pakistan da Afghanistan.

Wannan ya biyo bayan jerin shawarwari da aka yi a Islamabad tsakankanin PM kasar Nawaz Shariff, da shugaban Afghanistan Ashraf Ghani, da wasu manyan jami'an Amurka da na China. An yi ganawar ce a gefen taron shekara shekara na yanki kan batun Afghanistan.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka jiya Laraba, ta ce Afhanistan ce take jagorancin taron, ba tareda ta tabbatar da cewa za'a ci gaba da shawarwarin sulhu tsakanin kasashen biyu ba makon gobe.