‘Yan sanda a Spain sunce mai yiwuwa direban da ya rafkawa mutane mota suna tafiya da kafa a kan titin Barcelona ranar alhamis ya arce, sabanin rahotannin da aka bayar tun farko cewa direban na daga cikin wadanda aka kashe a irin wannan harin bayan ‘yan sa’oi a wani gari dake kusa.
Ana kyautata zaton Younes Abouyaaqoub mai shekaru 22 dan asalin kasar Morocco da ‘yan sanda k enema ruwa a jallo, shine shugaban kungiyar da ta kai hari a Barcelona da kuma wani birni a Cambrils.
A halin da ake ciki kuma, ministan harkokin kasashen ketare na kasar Jamus Sigmar Gabriel ya ziyarci Las Ramblas Boulevard yau asabar domin ajiye furanni a inda ake tunawa da mutanen da suka rasa rayukansu a Barcelona.
Gabriel yayi kira da a kara hada kai a kasashen turai da kuma sauran kasashen duniya a yaki da ta’addanci.
Mun sani ‘yan ta’adda na kokarin cusa tsoro da yayata tashin hankali. Mun fuskanci haka bara a kasuwar Kirsimeti dake birnin Berlin. Muna bukatar taimakon wadanda harin ya shafa da danginsu yanzu. Banda haka kuma, muna bukatar kara hada kai a kasashen turai, kamar yadda muka yi a lokutan baya. Sai dai abin takaici shine, babu yadda za a iya tabbatar da kariya daga wadannan matsoratan ‘yan kisan. Abinda ya kamata mu fahimta ke nan.