Coronavirus: Ko Za'a Soke Wasannin Olympics Na 2020?

Kwamitin shirya gasar wasannin Olymipcs na kasa-da-kasa na fuskantar karin suka daga 'yan wasan motsa jiki akan kudurinsa na gudanar da wasannin motsa jiki na Olympics na shekarar 2020 a birnin Tokyo kamar yadda aka tsara, duk da annobar cutar coronavirus da ake fama da ita.

A lokacin wani taro ta wayar tarho da jami’an hukumar Olympics da kuma wakilan ‘yan wasan motsa jiki daga sassa badam-daban suka yi, shugaban kwamitin Thomas Bach, ya ce babu wani shiri na soke gasar wasannin da aka tsara farawa daga ranar 24 ga watan Yuli zuwa 9 ga watan Agusta ya zuwa yanzu.

Zakaran da ya lashe gasar tukin kwale-kwale har sau hudu daga Birtaniyya, Mathew Pinsent, ya bayyana kalaman Bach a matsayin “rashin nuna damuwa akan halin da ake ciki” a shafinsa na twitter, inda yayi kira ga kwamitin da ya soke gudanar da wasannin. Pinsent ya ce bukatar bin umarnin gwamnatoci na guje wa cunkoson jama’a ba zai taba zama daidai da ka'idodin atisayen wasannin motsa jiki da tafiye-tafiye ba.

Sauran sanannun ‘yan wasa su ma sun goyi bayan ra'ayin Pinsent akan shirin wasannin na Tokyo.

Yawaitar yaduwar cutar coronavirus (COVID-19), ta tilasta wa hukumomin Olympics na kasashe a fadin duniya soke wasannin neman gurbi a gasar ta Tokyo, haka kuma lamarin ya shafi atisayen ‘yan wasa da tsarin shirye-shiryensu.