A yau Laraba an dauki sabbin matakan hana zirga zirga a Malaysia, kamar yadda aka fara a kasashen kungiyar Tarayyar Turai, inda aka hana ‘yan kasashen waje shiga kasashen, yayin da gwamnatoci suke kokarin hana yaduwar annobar cutar coronavirus.
An tabbar da mutum sama da 500 sun kamu da cutar a Malaysia, kana za a killace su tsawon makonnin biyu.
A Saudi Arabiya, jami’ai sun fadawa kamfanoni masu zaman kansu subar ma’aikatansu su rinka aiki daga gida idan zai yiwu, kana kuma wadanda suke zuwa wurin aikin to su dauki matakai na ba da tazara a tsakaninsu.
Tuni wasu kasashe suka dauki wadannan matakan don hana cudanyar mutane a wurin taruwar jama’a.
Kasashen Italiya, da Spain, da kuma Faransa yanzu haka suna karkashin tsananin hana zirga-zirga yayin da suke fama da adadi mai yawa na wadanda suka kamu da cutar a duniya.
Facebook Forum