Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakan Da Nahiyar Turai Ke Dauka Kan Coronavirus


Wani likita kenan yayin da yake jiran isowar karin mara sa lafiya a kasar Jamus
Wani likita kenan yayin da yake jiran isowar karin mara sa lafiya a kasar Jamus

Kungiyar Tarayyar Turai za ta rufe kan iyakokinta ga duk wani bako na tsawon kwanaki 30 tun daga yanzu, a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar murar Coronavirus.

Ganin mutum guda ne kawai sabon kamuwa da cutar a Wuhan na kasar China a jiya Talata, yanzu nahiyar Turai – musamman ma kasar Italiya, ita ce inda cutar ta fi addaba a duniya.

Daga cikin adadin mace-mace wajen 7,500 a duniya baki daya sanadiyyar cutar murar ta coronavirus.

Kasashen Spain da Faransa ne su ka zo na biyu da na uku a nahiyar ta Turai. Mutanen kasashen uku duk an killace su ala tilas.

Hasali ma, a kasar Italiya, duk wanda ya fito kan titi, muddun bai da wata kwakkwarar hujja, zai fuskanci dauri da kuma tara.

Kasar Belgium ma ta ayyana dokar hana kara kaina, kuma duk wanda ya kai shekaru 70 zuwa sama, ba shi ba fitowa waje a Serbia, ganin cutar ta fi kama tsofaffi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG