Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasuwar Hannayen Jari Na Fuskantar Barazana


Wani mai zuba hannun jari wanda ransa ya baci bayan da ya samu labarin halin da kasuwar hannayen jarin ke ciki.
Wani mai zuba hannun jari wanda ransa ya baci bayan da ya samu labarin halin da kasuwar hannayen jarin ke ciki.

Kasuwar hannayen jari ta sake faduwa saboda fargabar Coronavirus, yayin da aka samu faduwa a babbar kasuwar hannun jarin kamfanoni ta Amurka da aka fi sakawa ido Dow Jones.

Ta rasa duk ribar da ta samu tun daga ranar da shugaban kasa Donald Trump ya hau Mulki a watan Janairun shekarar 2017.

Yawancin kasuwannin Asiya sun yi ‘kasa da kashi 2 zuwa 6 bisa dari, wadanda ke Turai kuma sun fadi da kashi 4 zuwa 6 bisa dari, sai kuma na Amurka wadanda suka fadi da kashi 7 zuwa 10 bisa dari.

Wasu lokuta Trump kan yi tunkaho da ribar da kasuwar hannayen jari ta samu, a matsayin matakin dake nuna ci gaban tattalin arziki karkashin shugabancinsa.

Amma kasuwar Dow Jones ta rufe da maki 19,898, wato ‘dan banbanci kadan da maki 19,827 wanda ta rufe da a lokacin da Trump ya hau Mulki.

Ya zuwa yanzu dai kasuwannin sun kwashe makonni suna faduwa, sakamakon bullar cutar Coronavirus.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG