“Mun gaza samun nutsuwa. Mun kasa yin amfani da damar da muka samu, sannan ga rashin kyawun fili, idan za a fadi gaskiya.” Messi ya ce kamar yadda kamfanin dilllancin labarai na AP ya ruwaito.
Ya kara da cewa, “amma dai mun gaza samun nutsuwa sannan muna ta hanzari. Wannan kuma wani abu ne da Chile ta yi kokarin samu a lokacin da suka farke kwallon da muka ci."
"Dangane da bugun fenarti, gaskiya ban yi tsammani ya kamata a bayar ba, amma dai gaskiya ta sauya wasan baki daya.” In ji Messi.
A rukunin B, Neymar ya ci wa Brazil kwallo ta bugun fenarti a karawar da suka yi da Venezuela inda aka tashi da ci 3-0.
Wannan shi ne wasan farko na rukukin na B da aka buga ranar Lahadi, wanda hakan ya ba Brazil damar fara wa da kafar dama a kokarinta na kare kofin gasar da take rike da shi.
Ba a abokantaka a fili, Suarez ya fadawa Messi kan karawarsu a gasar Copa America
Your browser doesn’t support HTML5