Argentina ta zama kasa ta farko da ta kai zagayen dab da na kusa da na karshe a gasar cin kofin Copa America, bayan zura kwallo da Lautaro Martinez ya yi ana dab da tashi wasa da ya basu nasara da ci 1-0 a rukunin A a kan Chile a ranar Talata.
Sai dai masu rike da kofin sun jira zuwa minti na 88 domin samun nasara.
Bayan da Lionel Messi ya dauko kwana da Giovani Lo Celso ya buga kwallon da karfi inda mai tsaron raga na Chile Claudio Bravo ya tare sai Martinez ya tsinci kwallon a sadaka ya buga ta da karfi cikin raga.
Alkalin wasa ya bayar da kwallon da Agrentina ta zura bayan da aka duba na’urar VAR.
Argentina ce ta daya a rukunin A da maki shida bayan wasanni biyu da ta buga, yayin da Canada ke da maki uku a matsayi na biyu bayan nasarar da tayi a kan Peru da ci 1-0 a ranar Talata.
Chile da Peru kowanen su na da maki daya.
Rashin nasarar da Chile tayi a jere a kan Argentina a gasar cin kofin Copa America ya karu zuwa wasanni 30.
Chile ta lashe gasar Copa sau biyu amma ba ta taba doke Argentina a lokacin gasar ba, inda ta samu nasara a bugun fenariti a wasan karshen na 2015 da 2016.
Reuters