Kwallon da Jefferson Lerma ya zura a minti na 39 ya ba su nasara ci 1-0 a dare ranar Laraba kuma za su buga wasan karshe da masu rike da kofin, Argentina, a ranar Lahadi mai zuwa.
An dai baiwa Daniel Munoz jan kati ne a karshen zagayen farko na wasan saboda gwiwar hannun da yasa ya bugi wani dan wasa wanda hakan ya kai ga ba shi katin gargadi na biyu.
Duk da Uruguay ke rike da kwallo da kashi 61.9%, Colombia ta dage inda ta rike wasan da ta samu damar kai wa wasan karshe a karon farko, tun bayan da ta lashe kafin Copa daya tilo a matsayin mai masaukin baki a shekarar 2001.
Colombia ta ci gaba da rike kambunta nayin wasanni 28 ba tare da an doke ta ba, wanda ya fi na 1992-94 da kuma mafi tsayi a jere a gasar kwallon kafa ta kasa da kasa.
Argentina, mai rike da kofin za ta fafata da Colombia a Miami Gardens da ke jihar Florida, a wasan karshe na gasar.
Albiceleste na neman lashen kofin Copa karo na 16 kuma suna neman su yi daidai da Sipaniya daga 2008-12 a matsayin kasashen biyu da suka lashe manyan kofuna uku a jere.
Uruguay za ta hadu da Kanada a wasan gurbin neman na uku da za su buga a Charlotte a ranar Asabar.