Uruguay ta doke Brazil da ci 4-2 a bugun fenerati a ranar Asabar, bayan da aka bai wa dan wasanta jan kati suka koma 10 a karawar da su ka yi canjarus 0-0 a filin wasa na Las Vegas da ke Amurka.
Wannan nasara dai ta bai wa Uruguay damar tsallaka wa zuwa wasan kusa da na karshe, inda za su kara da Colombia a ranar Laraba.
An dakatar da Vinicius Jr na Brazil, kuma ya kalli wasan daga cikin ‘yan kallo, inda aka nuno shi ya zaku Brazil ta zura kwallo.
‘Yan wasan Dorival Jr sun yi ta kokarin samar da damarmaki duk da damar mutum daya da suka samu a karshe wasan zagaye na biyu lokacin da aka bai wa Nahita Nandez na Uruguay jan kati.
Mai tsaron gida na Uruguay Sergio Rochet ya buge feneratin da Eder Militoa na Brazil ya buga ta farko, yayin da abokin wasansa Douglas Luiz ya bugi raga ta fita, wanda hakan ya bai wa Uruguay nasara.
Ko da yake mai tsaron gida na Brazil Alisson Becker ya kade feneratin da Jose Maria Gimenez ya buga.
Sai dai Manuel Ugarte ne ya buga feneratin ta karshe da ta bai wa Uruguay damar zuwa zagayen kusa da na karshe, inda take neman lashen kofin Copa America na 16.
A ranar Talata ne Canada za ta buga wasan kusa da na karshe da Argentina, wanda wannan ne zuwan ta na farko irin wannan mataki da take fatan samun nasara a kan mai rike da kofin.
Dandalin Mu Tattauna