A wani zama da ake ganin zai zamanto sauraren bahasin da zai kafa tarihi, wanda za a yada ta kafar talbijin, tsohon lauyan shugaba Donald Trump, Michael Cohen, zai gurfana a gaban wani kwamitin Majalisar Wakilan Amurka a yau Laraba.
Cohen zai ba da bahasi ne kan wasu bayanai da suka shafi harkokin kasuwancin shugaba Trump, da kuma yadda kwamitin yakin neman zabensa ya gudanar da harkokinsa gabani da kuma bayan zaben 2016.
Cohen zai zamanto wani babban mai ba da shaida, tun bayan shekarun 1970s da aka ga badakalar nan da aka yi wa lakabi da “Watergate,” inda wani zai ba da shaida akan shugaba mai ci.
Daga cikin batutuwan da ake sa ran Cohen zai tabo, har da batun kudaden toshiyar-baki da aka bai wa wasu mata biyu domin su rufe bakinsu, matan da ke ikrarin sun yi mu’amulla ta lalata da Trump.