'Yan jam’iyyar Democrat a majalisar wakilan Amurka na shirin fito da wani kuduri wanda zai kalubalanci dokar ta baci ta kasa da shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana a kudancin iyakar kasar.
Kudurin wanda dan majalisar wakilai na jihar Texas, Joaquin Castro ne ya gabatar da shi, ana sa ran gobe Jumma’a za a gabatar da shi, kuma ta yiwu a kada kuri’a akan batun a majalisar tarayya zuwa tsakiyar watan Maris.
Shugabar majalisar wakilai, Nancy Pelosi, ta fidda wata wasika jiya Laraba tana neman 'yan majalissar daga jam’iyyar Democrat da Republican su sanya hannu a matsayin masu goyon bayan matakin, ta kuma ce matakin zai sami karbuwa da sauri.
A makon da ya gabata ne Trump ya ayyana dokar ta baci a bakin iyakar Amurka da Mexico bayan da ‘yan majalisar dokoki suka kada kuri’a akan wan ikudiri da ya amince a ware kudi kusan dala biliyan 1.4 don tsaurara matakan tsaro a bakin iyakar amma basu biya bukatar da dala biliyan 5.7 da shugaban ya nema.
Facebook Forum