KANO, NIGERIA - Ofishin ya ce daga watan Janairun bana zuwa karshen watan jiya na Maris ya karbi korafe-korafe da suka shafi cin zarfin mata a cikin gidaje da kuma yara kanana da yawan su ya kai kimanin dari uku.
A cikin wani rahoton watanni uku na farkon shekara da hukumar ta wallafa, ta ce adadin ya kunshi matsalolin da suka shafi zamantakewa tsakanin ma’aurata, da batutuwan da suka shafi yara, kamar aikatau, fyade da kuma tallace tallace.
Malam Shehu Abdullahi dake zaman kodinatan hukumar a shiyyar Kano ya ce abin damuwa ne ainun yadda zamantakewar ma’aurata ke kara dagulewa lamarin dake kara jefa makomar yara cikin yanayin rashin tabbas.
A cewar, Malam Shehu Abdullahi, binciken hukumar kare hakki na kasar ta Najeriya ya nuna tsadar rayuwa da shiga kafofin sadarwa na sada zumunta ta wayoyin hannu na daga cikin dalilan dake barazana ga zamantakewar ma’aurata a yanzu.
Alkaluman rahotan watanni ukun farko na wannan shekara ta 2022 daga ofishin shiyyar Kano na hukumar kare hakkin bil’adaman ta Najeriya ya koka kan yadda hukumar ba ta samun rahotannin al’amuran dake faruwa a tsakanin mazauna karkara, la’akari da cewa, batutuwan da ke kunshe cikin wannan rahotan wadanda suka wakana ne a birnin da kewayen Kano.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5