Kungiyar Amnesty International mai fafutukar kare hakkokin abil adama ta bayyana damuwa game da wasu matakan da jami’an tsaron kasar Ghana suka dauka akan fararen hula da ‘yan jarida, abin da yayi sanadin asarar rayuka tare da jikkatar wasu. Kungiyar na jawabin ne yayin da ta ke gabatar da rahotonta na shekara shekara ai nda ta bukaci da gwamnati ta dau matakai domin ganin ta kare hakkokin ‘yan kasa.
A bara ne wasu dakarun soja suka bude wuta akan wasu mutanen Zangon Ejura da ke jahar Ashnati yayinda su ke zanga zangar nuna damuwarsu bisa mummunar kisar da aka yi ma wani saurayi, Muhammad Kaaka, da aka ce mamban kungiyar matsin lamba ta FIXTHECOUNTRY ne.
Mutani biyu ne suka rasa rayukansu kazalika wasu suka jikkata sakamakon matakin da jami’an tsaron suka dauka. Mallam Usama Armiyau , mai tattaro matasan kungiyar matsin lambar ta Economic Fighters League yayi marhaban da kiran da Amnesty International ta yi ma gwamnati.
Kodinatan raya cigaban Zango da tsakiyar birane kana lauya mai kare hakkokin bil Adama, Hon Ben Abdallah Banda, ya ce gwamnati ta bai wa iyalan wadanda suka kwan babu sakamakon harin da sojoji su ka kai ma falaren hulan zangon Ejura diyya tare da tantance wadanda suka jikkata domin samar musu da diyyar da ta dace.
To sai dai ba anfani da karfi fiye da kima akan fararen hula kadai ne kungiyar ta yi Allah wadai akai ba, har da cinkoson fursunoni a gidajen yari, abinda mataimakin shugaban babban gidan yarin Kumashi, Mallam Usman ya gaskata
Kungiyar Amnesty International ta kuma ce cin zarafin mata ya karu, kazalika hare hare akan masu luwadi da madigu ya tsananta, tun lokacin da aka gabatar da kudirin haramcin luwadi da madigu a Majalisar Dattawa da tilasta mutane ficewa matsugunansu ya sanya jama'a da dama cikin mawuyacin hali akasar.
Saurari cikakken rahoton Hamza Adams