KANO, NIGERIA - Hukumomin kwalejin sun rike takardun daliban ne saboda rashin biyan kudaden makaranta daga bangaren gwamnati.
A shekara ta 2017 ne gwamnatin Kanon ta dauki nayin wasu ‘ya’yan jihar su dari, 60 mata, 40 maza domin su yi karatu a kwalejin wadda ake kira "Digital Bridge Institute" a fannoni daban daban na nazarin fasahar sadarwa.
Hakan dai na daga cikin matakan da gwamnatin ta ce tana dauka na samar da guraben karatu ga ‘yan jihar a kwalejoji da jami’o’i dake koyar da darrusa na musamman da su ka dace da kalubalen zamani.
Sai dai fiye da shekaru 2 da kammala karatun su, a kwalejin ta Digital Institute har yanzu gwamnatin ba ta kai ga biyan kudaden karantun daliban ba, lamarin da ya sanya mahukunta kwalejin suka rike takardun shaidar karatu na daliban.
Da Muryar Amurka ta tuntubi Dr. Mariya Mahmud Bunkure kwamishina a ma’aikatar kula da harkokin ilimi mai zurfi ta jihar Kano, ta ce shirin daukar nauyin karatun wadannan dalibai an tsara shi ne a ma’aikatar yada labarai, don haka ba ta da masaniya game da halin da ake ciki.
Dangane da haka ne Muryar Amurka ta bukaci jin ta bakin kwamishinan yada labarai Comrade Mohammed Garba, amma har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto bai kai ga amsa kiran wayar tarho ba, kuma bai ce uffan ba ga rubutaccen sako da muka tura masa.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari: