Cin Hanci da Karbar Rashawa Haramun Ne!

Debo Adeniran

Hukumar hana cin hanci da karbar rashawa ta Nigeria tayi kira ga shugaban kasa da yaki amincewa da duk wani matakin da ake shirin dauka na fadada hanyoyin karbar hanci da cin rashawa.
Shugaban hadin gwiwar hukumomin hana cin hanci da karbar rashawa ta Nigeria(CA-COL) yayi kira ga shugaba Goodluck Jonathan da kada ya sanya hannu a kan daftarin matakan da ake bada shawarar ya dauka domin taimakawa jami’an Gwamnati samun sukunin bude Asusun ajiyar kudi a Bankunan kasar waje.

Debo Adeniran, ya bayyana cewar idan har kudurin dokar ya sami sa hannun shugaban kasa, ke nan hukuma ta amince da hada-hadar da ake yi da kudin haram, sannan kuma haka zai karfafa bazuwar ayyukan ta’addanci a Nigeria da wasu sassa na duniya.

Yace “Muna kira ga shugaba Jonathan da kada ya amince da kudurin ya zama doka, idan har har yana son ‘yan Nigeria su amince da irin matakan da yake dauka domin dakile hada-hada da kudaden haram dake karfafa hanyoyin samar da kudaden ayukan ta’addanci.”Adeniran ya kuma kara da cewa” cin hanci da karbar rashawa zai karfafa a tsakanin jami’an Gwamnati idan har aka sake shirin baiwa jami’an damar ajiya a bankunan kasar waje; kuma hakan tamkar karfafa gwiwar masu hada-hada da kudaden haramun ne da kabbama ayyukan ta’addanci, haka kuma ka iya janyo babbar matsala.”

Dokokin Nigeria sun hana ma’aiakatan Gwamnati mallaka da bude asusun ajiyar bankin kasar waje, sai dai ‘yan majalisar dokokin Tarayya sun fara muhawara da tattauna kudurin dokar yin gyaran fuska game da kudurin dokar, domin baiwa ma’aikatan gwamnatin sukunin bude ajiya a bankunan kasar waje.

Anji Adeniran yana cewa ana yawaita zargin jami’an Gwamnati da laifin yin tabargaza da dukiyar jama’a ta hanyar bude asusu a bankunan kasar waje duk da dokar hana yin hakan da yanzu ake da ita wadda ba’a aiki da ita.

Dalilin da yake sawa da yawa daga cikin jami’an Gwamnati basa iya yin safarar takardun kudi zuwa kasa da kasa, shine saboda dokoki masu karfin da ake dasu a mafi yawan kasa da kasa. Kuma ana yawan kama masu karya dokar ana daurewa lokacin da suka nemi yin satar fage su fice da kudaden na haram, ko kokarin baiwa masu ajiya a Bankunan kasar waje kudin domin yin ajiya a bankunan kasar waje.

Adeniran ya kara da cewa sun damu kwarai da jin cewa Nigeria na dab da amincewa dokar baiwa jami’an Gwamnatin damar bude asusun banki a kasar waje, domin hakan zai baiwa jami’an sukunin kwashe kudaden haram suna kwaiwa bankunan kasar waje suna boyewa.