Hukumar Alhazan ta jihar Gombe ta bayyana gamsuwarta dangane da yadda aka shirya jigilar alhazan jihar zuwa kasar Saudiya da yadda aka dawo da su. Shugaban hukumar Injinia Sale Mohammed Umar wanda kuma har wayau shi ne Mai-Kaltungo ya bayyana hakan a wata fira da ya yi da wakiliyar Muryar Amurka Sa'adatu Fawu a Kaltungo.
Mai-Kaltungo ya ce ranakun da aka basu na tashi da na dawowa su ne aka bi. Babu wani canji ko sake masu lokutan tashi.Ya ce sun tafi cikin jirage hudu kuma sun dawo cikin jirage hudu. Ya ce lamarin ya sa sun dawo da sauri. Lamarin ya taimaka masu. Ya ce idan an kwatanta aikin hajjin bana da na da babu shakka na wannan shekarar shi ya fi kayatarwa domin gwamnan jihar Ibrahim Dankwambo ya basu duk abubuwan da suka bukata tun daga nan Najeriya har a kasar Saudiya inda ya samar masu da gidajen haya dap-dap da wuraren da zasu yi aikin ibada. Bugu da kari sabbin alhazai suka tafi da su kuma an yi masu bita yadda ya kamata. An koya masu irin dabi'un da zasu yi a can kasa mai tsarki. Ya ce basu samu wata matsala da kowa ba kuma sun samu malaman kwarai da suka yi masu jagoranci nagari.
Bisa ga lafiyar alhazan, basaraken ya ce mutum daya ne ya yi rashin lafiya domin kafin su tashi likitocinsu sun tantancesu sosai. Ya ce akwai shirye-shirye da yawa da aka yi shi ya sa aikin ya samu gagarumar nasara wannan shekarar fiye da shekarun da suka wuce.
Daga bisani ya bada shawarar a rage dadewar alhazai a Saudiya. Da kwanaki arba'in da biyu suka yi , amma wannan shekarar sai gashi an sa sun yi kwanaki arba'in da biyar.
Sa'adatu Fawu nada karin bayani.