Rundunar ta kai samame a wani katafaren kamfanin inda ake sarafa jabun barasa iri daban-daban da wasu lemuka iri-iri. Rundunar ta kama manajan kamfanin ta kuma kwace wasu injina da kamfanin ke anfani da su. Kamfanin na wata karamar hukumar Njaba ne.
Alhaji Mohammed Musa Katsina shi ne Kwamishanan 'yansandan jihar kuma ya yiwa Muryar Amurka bayani. A cikin bayaninsa kwamishanan 'yansandan ya ce mutumin mai suna Ume yana sarafa barasa na kamfanoni iri-iri da ma lemun sha duk da sunan kamfanonin dake yinsu. Wato yana anfani da sunayen kamfanoni daban-daban yadda jama'a zasu dauka kamfanonin ne suka yi su. A kowane wata ya kan fitar da katan kusan guda dubu. Wadannan abubuwan da yake sarafawa ana sayar dasu a jihohin kudu maso gabas da na arewa da ma wasu manya-manyan garuruwa. Bai tsaya nan ba. Yana ketarewa da su zuwa kasashen Togo da Benin.
Alhaji Muhammed ya kara da cewa kamfanin na kuma sarafa jabun magunguna da suka hada da amala na malariya da na mura da dai sauran wasu kananan cututtuka. Mr. Umenka manajan kamfanin mai shekaru 68 ya ce barasar da ya keyi tana da kyau kuma tana da araha. Idan ya kai kasuwa mutane suna samun rangwame shi ya sa suka sarafa barasar da sauran lemunmuka domin wadanda basu da karfi su samu abun saye. Ya ce kayan kasashen turai suna da tsada sosai amma nashi nada araha ga kuma kayatarwa. Ya ce kamfaninsa nada ma'aikata goma sha tara wadanda rayuwarsu ta dogara ne ga kamfanin.
Wani basaraken yankin ya ce ya samu labari 'yansanda da dama da 'yan jarida sun shigo kasarsa shi ne dalilin da ya sa ya zo ya gane ma idanunsa. Ya ce a zahirin gaskiya ya ga abun mamaki kuma abun da kamfanin ke yi bashi da kyau domin kusan shekaru takwas ke nan yana wannan aikin jabun. A gaskiya masarautarsa bata sani ba sai daga baya.
Lamido Abubakar nada karin bayani.