Da ya ke jawabi yau a birnin Ikko wurin kaddamarwar, Ministan Kudin Nijeriya Alhaji Lawal Ingawa y ace wannan tsarin na Takaful ya banbanta da nay au da kullum. Y aba da misalign cewa babu wani ajiyayyen kamfanin insuran da ya mallaki tsarin saboda jama’a ne da su ka hada kansu za su rinka tara kudi karkashin wannan tsarin na Takaful don su rinka taimakon juna idan bukatar hakan ta taso. Hakazalika, Ministan y ace wannan tsarin bai da kudin ruwa tsakanin masu shi, saboda za a rinka raba ribar
kasuwancin ne daidai da abin da mutum ya ajiye. Haka kuma ba za a yi kasuwancin da bai halatta ba da kudin. Sannan kuma, in ji Ministan, kudin da ka zuba na nan a matsayin kudinka ko da kuwa ka fita daga tsarin.
Da wakilinmu, wanda ya turo mana da rahoton ya tambaye shi irin rawar da gwamnati za ta iya takawa sai Ministan ya ce dayake sha’ani ne na haduwar jama’a gwamnati ba za ta shigo sosai ba. Za ta samar da yanayin da zai taimaka ne kawai amma za ta bar jama’a su tafi da harkokinsu yadda su ke so; saidai hukuma za ta bi kadi ma duk wanda aka kwara ko kuma ya ke da korafi.
Shi ma Kwamishinan Inshora na Kasa, Mr. Fola Daniel ya ce ba Musulmi ne kadai za su iya amfani da wannan tsarin ba. Mai bin kowane irin addini na iya amfani da tsarin muddun ya cika sharuddun da jama’a su ka gindaya. Ya kara da cewa za a yi hukunci irin na Musulunci ne ga duk wanda ya saba ma wannan tsarin.