Shugaban Syria, Bashar al Assad, ya ce cimma matsayar tsagaita wuta, za ta yi wuyar aiwatarwa, ya kuma zargi Turkiyya da Saudi Arabia da zama karnukan farautar manyan kasashen duniya.
WASHINGTON DC —
A wani jawabi da ya yi jiya a Damscus, Assad ya ce Turkiyya da Saudi Arabia, sun jima suna so su tura dakarunsu zuwa kasarsa, ya kuma jaddada cewa watannin kadan da fara yakin na Syria da aka kwashe shekaru biyar ana yi, yakin ya jirkice ya koma na kasa da kasa.
Kasashen Turkiyya da Saudiyya sun kasance suna cikin dakarun hadin gwiwar da Amurka ke jagoranta wajen fatattakar kungiyar IS a Syria, suna kuma da burin su tura dakarun kasa.
A ranar Asabar din da ta gabata, Turkiyya ta kaddamar da wasu hare-haren sama a kan iyakar kasar, inda mayakan Kurdawa ke zaune a arewacin Syrian, tare da yin gargadin cewa mayakan na Kurdawa su janye, ko kuma su fuskanci mummunan martani.