A yau Alhamis ne ake sa-ran mutumin da ake zargi da kisan mutane 11 a wata masujadar Yahudawa dake garin Pittsburgh dake nan Amurka zai bayyana gaban wata kotun Tarayya inda ake zarginsa da laifuka 44 ciki harda na kisa da kiyayya.
WASHINGTON D C —
Tun jiya Laraba ne wani gungun masu yanke hukunci suka tuhumi Robert Bowers, dan shekaru 46 da haihuwa da laifin kai harin na ranar 27 ga watan Oktoba a masujadar Tree of Life dake Pittsburgh.
A lokacin da yake bayyana zarge-zargen, babban Attorney-Janar din Amurka Jeff Sessions ya ce “laifukan da ake zargi sun yi munin da ya wuce gaban fahimtar bil’adama kuma sun yi mummunan sabawa tsarin kasar. Ya cigaba da cewa, don haka, wannan lamarin ba kawai ga wadanda abin ya shafa da iyalansu yake da muhimmanci ba, har ma da birnin Pittsburgh da kasar baki daya.”
A yau Alhamis dai ana cigaba da zaman makokin juyayin wadanda aka kashe a yayinda ake jana’izar wasu da aka kashen da suka hada da Bernice da Sylvan Simon, da kuma Dr. Richard Gottfried.