Shugaban gwamnatin Li Keqiang shine ya bayyanar da wannan mataki a yau Talata a wurin bude wani taron majalisar dokokin da shekara a birnin Beijing.
Li ya fadawa ‘yan majalisar cewa masu aiwatar da tsare tsaren kasa sun auna samun bunkasar tattalin arziki ta kashi 6 zuwa shida da digo biyar a wannan shekara, hasashen da ya dan yi kasa a kan na bara na kashi 6.5 a bara.
Tattalin arzikin China, wanda shine mafi girma na biyu a duniya, ya samu bunkasar kashi 6.6 a shekarar 2018, tafiyar hawainiyar da tattalin ya huskanta a cikin shekaru 30 dangani da rashin sayin kaya a gida da kasashen waje da kuma mummunar yakin ciniki tsakaninta da Amurka.
Shugaban gwamnatin yace gwamnati zata yi rangwamin dala biliyan 298 na harajin masana’antu da kudaden biyan insharan jama’a kuma ta rage harajin kaya a kan masana’antun ta kashi 16 zuwa 13 cikin dari.
A hali da ake ciki kuma Beijing ta rattaba hannu a kan dala biliyan 177 da zata kashewa ayyukan soji a wannan shekara, lamarin da ya kai ga karin kashi 7.5 cikin dari.