Kanfanin kasar China zai soma aikin hako Uranuim à arewacin kasar, lamarin da zai sanya Nijar ta zama kasa ta uku mafi ma'adinan uranuim a duniya.
Sai dai kungiyoyi gwagwarmaya à Nijar sun bukaci jagororin kasar su soke duk wani lasisi na hako ma'adinan Uranuim a cikin kasar duba da yadda aka shafe shekaru kusan 50 ana fitar dashi amma kuma Nijar bata anfana da komai ba.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin mulkin sojojin Nijar karkashin jagorancin Abdurahmane Tchaini suka raba gari da kasashen yamma musan man Faransa da ta yi wa Nijar mulkin mallaka.
Ana dai kallon wannan yunkurin na kasar China na kyautata dangantaka da jagororin mulkin sojan kasar ta Nijar domin karfafa tasirin ta a kasar ta Nijar.
Nijar dai tana daga cikin kasashen dake fuskantar matsalar gurbata muhalli inda yake haifarwa kasar ambaliyar ruwa da kwararowar hamada da kuma takaituwar filayen noma da kiwo to sai dai kungiyoyin kare muhalli na gargadi dangane da gurbata muhalli daga aikin hako ma’adinai da kanfanonin ke aikatawa inda suka yi kira ga hukumomi da su sanya ido akan kanfanonin.
Saurari rahoton Hamid Mahmud:
Your browser doesn’t support HTML5