Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ta bakin gwamnan jihar Borno Ibrahim Shettima ya roki iyayen 'yan matan da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace yau fiye da kwanaki 500 da su kara hakuri.
Ranar Alhamis da ta wuce 'yan matan suka cika kwanaki dari biyar a hannun 'yan ta'adan. Saboda haka shugaba Buhari ya umurci gwamnan jihar Borno ya kira iyayen ya basu hakuri tare da basu tabbacin cewa nan ba da dadewa ba zasu sadu da 'ya'yansu.
Shugaban kasa Buhari yana kan bakansa zai kwato 'yan matan. Matsalar, inji shi ta zo kusan karshe.
Kanar Rabe Abubakar mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya yace suna iyakacin kokarinsu su tabbatar duk wadanda suke hannun 'yan ta'adan tare da 'yan matan Chibok an kubutar dasu.
Dr Emma Shehu daya cikin shugabannin masu fafitukar ganin an ceto yan matan yace yanzu suna da kwarin gwiwa cewa za'a ceto 'yan matan saboda gwamnatin yanzu tana kokari matuka ba kamar ta Jonathan ba.
To saidai wasu masu sharhi sun ce 'yan kungiyar fafutikar ganin an kubutar da 'yan matan wai yanzu sun fi maida hankali ne akan neman mukamai a gwamnati batun da Dr Shehu yace zargin banza ne.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5