Chelsea Ta Lashe UEFA Super Cup Bayan Da Ta Doke Villareal

'Yan wasan Chelsea suna murnar lashe kofin UEFA Super Cup

Dan wasan da ya fi haskawa a wasan shi ne, mai tsaron ragar Chelsea Kepa Arrizabalaga saboda kade fenariti biyu da ya yi.

Chelsea, wacce ta lashe kofin zakarun nahiyar turai, ta sake lashe kofin UEFA Super Cup, bayan da ta doke Villareal da ci 6-5.

Kungiyar ta yi nasarar daga kofin ne bayan da aka tashi da ci 1-1 aka kuma kai ga bugun fenariti.

Dan wasan Chelsea Hakim Ziyech ne ya fara zura kwallo a ragar Villareal kafin daga baya ita ma ta farke kwallon, lamarin da ya kai ga karin lokaci da bugun fenariti.

Gerard Moreno ya zura kwallo a ragar Chelsea bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Dan wasan da ya fi haskawa a wasan shi ne, mai tsaron ragar Chelsea Kepa Arrizabalaga da ya shigo a matsayin canji, saboda kade fenariti biyu da ya yi, abin da ya ba Chelsea ta Ingila damar doke Villareal ta kasar Sifaniya a wasan karshen.

Arrizabalaga ya maye gurbin Edouard Mendy ne a wasan, abin da ya ba shi damar nuna bajintarsa.

Nasarar Chelsea na zuwa ne bayan da ta doke Manchester City a watan Mayu a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar turai a karo na biyu.