Duk da cewa ta sha kaye a hannun Chelsea a karshen makon da ya gabata, City ta yi saurin farfadowa a wannan kakar wasa bayan da ta samu maki 12 daga wasa takwas da ta buga.
Kwallayen Caglar Soyuncu da Luke Thomas suka katsewa United hanzari, duk da kwallon da Mason Greenwood ya zura.
Yanzu City wacce ta ba da tazarar maki 10 a saman teburin gasar, na da wasanni uku da suka rage mata a wannan kakar wasa.
Hakan na nufin City, wacce ta jima tana jira ta fara bikin lashe kofin, ta lashe gasar a karo na uku kenan cikin shekara hudu da suka gabata.
‘Yan wasan na Pep Guardiola sun taka rawar gani a wannan kaka, abin da ya kara masu kwarin gwiwar kai wa ga gaci.
Wannan shi ne kofi na 10 da Guardiola ya samu tun bayan da ya samu tun bayan da ya je City a shekarar 2016