Chelsea Ta Kai Wasan Karshe a Gasar UEFA

Dan wasan Chelsea, Callum Hudson-Odoi.

Sakamakon wannan wasa bayan doke Madrid da ci 2-0, na nufin ‘yan wasan Thomas Tuchel za su kara da Manchester City a Istanbul a wasan karshe na gasar ta Champions League.

Chelsea ta kai matakin wasan karshe bayan da ta lallasa Real Madrid da ci 2-0 a karawar semi-final a zagaye na biyu na gasar lashe kofin zakarun nahiyar turai.

Idan aka hada jimullar kwallayen wasannin biyu, ya zama Chelsea ta doke Madrid da ci 3-1.

A zagayen farko kungiyoyin sun yi kunnen doki da ci 1-1 a filin wasan Madrid da ke Spain.

Sakamakon wannan wasa na nufin ‘yan wasan Thomas Tuchel za su kara da Manchester City a Istanbul a wasan karshe a gasar ta UEFA.

Timothy Werner ne ya fara zura kwallo a minti na 18, sai Mason Mount ya zura kwallonsa a minti na 85 duk da ya zubar da wata babbar dama da ya samu a wasan.

Madrid dai ta fi yawan rike kwallo a wasan da kashi 73 cikin mintina 27 na farko kamar yadda kididdiga ta nuna.

A ranar Talata City ta doke PSG da jimullar kwallaye 4-1.

Hakan na nufin kungiyoyin gasar Premier League ne za su kara a wasan karshen, wanda za a yi ranar 29 ga watan nan na Mayu.

Madrid ta sha kaye ne duk da cewa ‘yan wasanta Sergio Ramos da Eden Hazard sun dawo buga wasa.