Wata zanga-zanga da ta barke a filin wasa na Old Trafford a Ingila, ta sa an dage karawar Manchester United da Liverpool a gasar Premier League.
Boren ya samo asali ne bayan da magoya bayan United suka fito don nuna adawarsu ga iyalan Glazers wadanda su suka mallaki kungiyar ta Manchester United.
A shekarar 2005, ‘ya’yan Malcolm Glazers su shida suka saye mafi aksarin hannayen jarin kungiyar, abin da ya ba su damar mallakar kungiyar.
Masu zanga-zangar suna nuna fushinsu ne, saboda nuna goyon baya ga sabuwar da gasar Super League da aka yi, wacce aka tsara za ta maye gurbin gasar Champions League – amma daga baya aka fasa.
Rahotanni sun ce dandazon mutane ya taru a kofar shiga filin wasan na Old Trafford inda aka tsara za a fara zanga-zangar da misalin karfe 2 na rana agogon Ingila.
An dai tsara za a fara wasan na United da Liverpool ne da misalin karfe 4:30 na yamma, amma daga baya kungiyar ta United ta ba da sanarwar cewa an dage wasan da misalin karfe 5:30.
Jami’an tsaro dai sun yi nasarar korar daruruwan masu boren daga cikin filin, wanda da ma an tsara babu wanda zai shiga saboda annobar coronavirus.