Kungiyar Kwallon kafa ta AS Roma da ke kasar Italiya, ta sanar da nada Jose Mourinho a matsayin sabon kocin kungiyar.
Roma ta fitar da sanarwa ce a ranar Talata a shafnta na Twitter gabanin a fara wasan kakar 2021-2022.
“Kungiyar na mai farin cikin sanar da cewa, ta cimma matsaya da Jose Mourinho don ya zama sabon kocin kungiyar gabanin a fara kakar wasa ta 2021-2022.” AS Roma ta wallafa a shafnta na Twitter.
Mourinho zai maye gurbin Paulo Fonseca ne, wanda zai kammala wa’adinsa a karshen wannan kaka ta 2020-2021.
Wannan ba shi ne karon farko da kocin dan asalin kasar Portugal zai horar da ‘yan wasa a gasar ta Seria A da ke kasar ta Italiya.
Ya taba zama kocin Inter Milan a tsakanin shekarun 2008-2010, inda ya kai kuniyar ga gaci.
Sallamar ta Mourinho da Tottenham ta yi, na zuwa ne bayan da ya kwashe wata 17 yana horar da 'yan wasan na Hotspur.
Dan shekara 58, Mourinho ya sha kaye a wasa 13 a gasa daban-daban da ake bugawa a kasar ta Ingila a wannan kakar wasa.
Wannan shi ne kaye mafi yawa da ya taba sha a tarihin aikinsa na horar da ‘yan wasa, kuma akwai rahotanni da suka nuna cewa ‘yan wasansa sun gaji da wata sara da ya dauko, ta yi musu fada a baina jama’a a duk lokacin da suka sha kaye.
A watan Nuwambar shekarar 2019, Mourinho ya karbi ragamar tafiyar da kungiyar daga hannun Mauricio Pochettino.