CENI Ta Shirya Tsaf Don Gudanar Da Zaben ‘Yan Majalisa Na 'Yan Nijar Mazauna Ketare a Ghana

Akwatunan jefa kuri'a

Hukumar zaben kasar Nijar ta CENI ta ce ta kammala shiri don zaben ‘yan majalisar dokoki na 'yan Nijar mazauna ketare wanda za a yi kasar Ghana da sauran wasu kasashe a ranar Lahadi 18 ga Yunin 2023. Jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki da MODEM Lumana sun shirya wani gangami na tallata ‘yan takararsu.

Shugaban kwamitin shirye-shiryen zaben ‘yan majalisa da za su wakilci ‘yan Nijar mazauna ketare da za a yi a Ghana, Dakta Maman Aminou Amadu Koundy, ya bada tabbacin cewa duk shirye-shiryen da suka dace na tafiya bisa tsari.

“Da dadewa mun riga mun samu kayan zabe kuma mun rarrabasu. Muna da sunayen mutanen da za su kada kuri’a a rumfanan zabe. Komai na tafiya daidai," a cewar Koundy.

DR. MAMAN AMINOU A. KOUNDY

Dakta Koundy ya kuma ce da karfe 8 na safe za a fara kada kuri'a a kuma kammala da karfe 7 na yamma a mazabu 113 da ke fadin Ghana, kuma cikin mutane 32,766 da suka yi rijista mutane 27,033 ne suka karbi katunan zabensu.

Yayin da zaben ke karatowa, wasu jam’iyyun siyasar Nijar sun shirya gangamin tallata 'yan takararsu.

A jawabin da yi na gabatar da ‘yar takarar jam’iyyar PNDS Hajiya Balki Hamidou Issaka a yayin wani taro da aka yi a birnin Kumasi, babban sakataren jam’iyyar ta kasa Foumakoye Gado, ya yi kira ga 'yan Nijar da su zabi Hajiya Balki domin kasancewar jam’iyyar ke da rinjaye a majalisar dokoki.

FOUMAKOYE GADO

Jam’iyyar Modem Lumana ma ta yi nata taron gangamin a kasuwar Garba da ke yankin Tsakiya, inda ta gabatar da ‘yar takararta, Hajia Aichatou Mayaki.

Hajiya Aichatou ta bayyana kwarin gwiwar cewa ‘yan Nijar mazauna Ghana za su kada mata kuri’a a matsayinta na mace.

AICHATOU MAYAKI - LUMANA

A shekarar 2016 ne dokar da ta ba ‘yan Nijar mazauna kasashen waje damar kada kuri’u a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki ta fara aiki, dokar ta kuma bada damar aika wakilai 5 daga ketare zuwa majalisar dokokin kasar mai kujeru 171.

Za a gudanar da makamancin wannan zabe a kasashe 15, ciki har da 12 daga nahiyar Afrika, 2 a Turai, da kuma Amurka.

Saurari rahoton Idris Abdullah cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

CENI Ta Shirya Tsaf Don Gudanar Da Zaben ‘Yan Majalisa Na 'Yan Nijar Mazauna Ketare a Ghana