Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Nijar Mazauna Kamaru Na Shirin Zaben 'Yan Majalisar Dokoki Na Bangare


Hukumar Zaben Nijar Ta Fara Gudanar Da Rajitan ‘Yan Kasar Dake Zama Kasashen Waje
Hukumar Zaben Nijar Ta Fara Gudanar Da Rajitan ‘Yan Kasar Dake Zama Kasashen Waje

An tsara gudanar da zaben ne a ranar 18 ga watan Yuni inda a Kamaru jam'iyyun siyasar Nijar da dama sun yi taro domin kaddamar da yakin neman zabe.  

YAOUNDÉ, CAMEROON, ‘Yan Nijar mazauna Kamaru sun haɗu ƙwansu da ƙwarƙwata, sun fito daga dukkan kusurwoyin kasar domin shiga zaben. Masu fafutuka na jam'iyyun siyasa daban-daban sun gudanar da taruka a gundumar Nkomkana da ke Yaoundé, babban birnin Kamaru.

Da farko dai mun halarci taron magoya bayan jam'iyyar PNDS TARAYYA mai mulki Inda aka gudanar da jawabai da kiraye-kirayen karfafa jam'iyyar shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum albarkacin zaben ‘yan majalisa na bangare.

Alhaji Sahabi Jihadi, daya daga cikin jagororin taron ya bayyana farin cikin sa kan yadda ‘yan ja'miyar suka amsa kira.

Shugabar matan PNDS Tarayya a Yaounde Hadjiya Kadi ita ma ta tofa albarkacin bakin ta musamman kan gudun mawar matan jam'iyar PNDS.

Haka kuma a bangaren jam'iyyar adawa ta MODEN FA LUMANA, ita ma ta hada taro a wannan rana.

A ranar 18 ga watan Yuni ne aka shirya gudanar da zaben.

Kasar ta Nijar na daya daga cikin kasashen Afirka da suka bai wa 'yan Kasar mazauna waje damar zabe a ƙasashen zaman su, sabanin wasu kasashen Afirka kamar Najeriya da Kamaru.

Saurari cikakken rahoto daga Mohamed Bachir Ladan:

'Yan Nijar Mazauna Kamaru Na sSirin Gudanar Da Zaben 'Yan Majalisar Dokoki Na Bangare.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG