Ce Ce Ku Cen Siyasa Ya Barke A Amurka

Cece-kuccen siyasa ya barke a tsakanin ‘yan takaran shugabancin Amurka zaben bana, watau Hillary Clinton da Donald Trump, inda suka kara kaimi wajen zargin juna biyo bayan bayanin takardun harajin dan takarar na Republican na shekarun 1995 da jaridar New York Times ta rawaito.

Wasu da ba a gano ko suwa nene ba suka aikawa jaridar takardun haraji inda Trump din ya bayyana cewa yayi asaran Dala milyan 916 a harakokinsa na kasuwanci a shekarar 1995 wanda hakan ya bashi hurumin dauke mishi biyan harajin na shekaru da yawa da suka biyo baya.

Wannan bayanin ya bayyana ne yan kwanaki kadan bayan da, a lokacin muhawsarar da suka yi ta makon jiya, Hillary Clinton ta caccaki Trump

harakokinsa na kasuwanci da kuma kin amincewarsa na ya bayyanar da harajin da ya biya na shekaru da dama.

Sai dai babu wani abu a cikin takardun da aka aikewa jaridar New York Times da ya nuna Trump ya sabawa dokokin haraji na Amurka tunda an yarda masu biyan haraji su nemi sassabci idan sun fuskanci wata asara a sana’oinsu ko aiyukkan da suke.