Kungiyar kare 'yan jarida ta duniya ta zargi gwamnatin Najeriya da garkame 'yan jarida da masu sharhi ta kafar sadarwa da masu aiki a kamfanonin jarida a sassa daban daban na kasar.
Kungiyar ta kira gwamnatin kasar da ta hanzarta ta sako mutane goma sha ukku da yanzu take tsare dasu a wurare daban daban da suka hada da 'yan jarida da masu sharhi ta kafofin sadarwa da masu aiki a jidajen jarida.
Kungiyar tayi allawadai da yadda jami'an tsaro ke cin zarafin 'yan jarida tare da nuna halin ko in kula lamarin da aka kwatanta da mulkin danniya na soja da aka taba yi a kasar inji Peter Nkanga wakilin kungiyar na Yammacin Afirka. Kungiyar ta kira Shugaba Buhari ya hanzarta ya kawo karshen wannan danyan aiki na razana 'yan jarida da hanasu yin aikinsu cikin walwala.
Kungiyar ta bada misalai. Ranar 21 na watan Satumbar wannan shekarar sojoji da 'yan sanda na musamman da 'yansandan farar hula ko SSS sun kama 'yan jarida goma da ma'aikatansu na wani kamfanin labarai dake kafar sadarwa da ake kira Watchdog Media a turance a birnin Benin dake jihar Edo. 'Yan jirdai sun je Benin ne domin zaben gwamna da za'a yi.
Jaridar tace 'yan jaridan an kamasu aka kuma tubesu aka barsu daga su sai kamfai kamar yadda Taiye Garrick edita din jaridar ya sanar.
To saidai a wata sanarwa da mai magana da yawun soji ya fitar Kanar Sani Usman washegari, yace sun samu rahotanni dake cewa wasu bata gari suna otel din ne a birnin Benin da zummar tada hatsaniya. Yace an samu mutanen da wasu kaya masu tada hankali hadda kayan zabe, amma bai yi wani cikakken bayani ba.. Sai dai har yanzu ba'a tantance 'yan jaridar ba. Amma jaridar Watchdog Media ta buga hotunan 'yan jaridan.
Ana zargin jami'an tsaro da tsare mutanen ba tare da barin 'yan'uwa ko abokanansu su gansu ba.
Wadanda aka kama sun hada da Tony Abulu, Richard Haley, Opara Uche, Handy Romeo Eze, Kelvin Toryila, Lanre Ogunleye, Balogun Ehigie, Kenneth Danpome da Joe Epi wanda ya kasance direbansu.
To saidai a wani abu mai ban mamaki ya fito daga kalamun shugaban kungiyar 'yan jarida reshen jihar Edo Mr. Roland Osakwe. Yace ya ziyarci mutanen da aka tsare kuma ya gano ba 'yan jarida ba ne saboda haka yace babu ruwan kungiyar da irin mutane dake shafawa 'yan jarida da aikin jarida kashin kaza. Ya kira duk masu kokarin zama sojin gona da sunan 'yan jarida domin samun kudi da su shiga taitayinsu.
A wani hannun kuma 'yansanda daga jihar Katsina sun fitar da sanarwar kama wani Jamil Mbai na mujallar Cliqq da wani marubuci a jaridar Reporters. Haka ma wani ya yi sharhi akan wai gwamnan Katsina ya sayi makara dubu ukku ya rabawa masallatai. Shi ma ba'a barshi ba an kamashi kamar yadda za'a ji a rahoton dake kasa.
Kwamishanan 'yansadna Katsina yace sun cafke Mbai ne da sauran mutanen bisa ga korafin da gwamnatin Katsina tayi akansu.
Haka ma 'yansanda suka tsare Bashir Dauda da Umar Faruq ranar 19 ga wannan watan akan sharhin da suka yi akan abun da Mbai ya rubuta ana zarginsu da taimakawa shi Mbai din.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.