Jiya shugaban Najeriya ya bude taron shugabannin masu masana'antu a Najeriaya da ake kira Manufacturers Association of Najeriya, a turance, na arba'in da hudu.
Yayinda yake jawabi shugaba Buhari ya yaba masu da irin gudummawar da suke bayarwa wajen gina tattalin arzikin kasar da inganta zamantakewar al'umma na shekaru da dama. Saka jarin da suke yi na gina masana'antu babbar shaida ce na bangaskiya da suke da ita kan kasar.
Shugaba Buhari yace gwamnatinsa zata hada hannu dasu su yi aiki kafada da kafada tare domin kai Najeriya gaba da manufa mai kyau da zata anfani al'ummar kasar. Yace gwamnati ta yaba da yadda suka taimaka wajen gina tattalin arzikin kasar.
Shugaban yace taron nasu ya zo daidai lokacin da kasar ke tunanen kirkiro da hanyoyi daban daban na samar da kudaden shiga. Saboda haka yace takensu na taron ya yi daidai. Taken taron kuwa shine "Rawar da Gwamanati Zata Taka Wajen Sarafa Kaya" Yace da faduwar farashin man fetur ko shakka babu gwamnatin nada rawar da zata taka na taimakawa masana'antu su habaka ta yadda zasu habaka tattalin arziki.
Faduwar farashin mai ya jawo wa kasashen dake sayar da mai koma baya musamman Najeriya wadda tattalin arzikinta ya kusa durkushewa gaba daya saboda dogaro ga man fetur kacokan. Wajibi ne gwamnati ta tashi tsaye ta hada karfi da karfe tare da masana'antu domin farfado da tattalin arzikin kasar. Kowa ya san masana'antu su ne kan gaba wurin gina arzikin kasa.
Shugaba Buhari ya cigaba da cewa su a gwamnatance suna kokarin su inganta hanyoyin sayen kayan da aka sarafa cikin gida. Haka kuma gwamnati na kokarin sake horas da dalibai su samu ilimin aikin masana'antu bisa abun da suka koya a makarantu. Abun nufi nan shi ne gwamnati zata gyara manhajar karatu da zai karfafa samun kwarewa a kan masana'antu.
Daga karshe shugaban ya gaidasu kan taronsu na arba'in da hudu kana ya kira su hada kai da gwamnati dangane da kokarin da gwamnati keyi yanzu ta ci nasara. Yace nan da 'yan watanni za'a kira wasunku ku taka rawa ta musamman wajen aiwatar da tsare tsaren gwamnati. Ya rokesu da su taimaka kasar tayi koyi da abubuwan da suka sani saboda inganta tattalin arzikin.