Daraktan ma'aikatar sasanta 'yan kasa Alhaji Shehu Shafa Kadiri Ummani shi yayiwa Muryar Amurka karin bayani akan kwamitin.
Yace kwamitin ya kumshi mutane iri iri da suka kware a fannoni daban daban tare da shugabannin kungiyar 'yan kwadago har ma da iyayen yara. Kwamitin zai binciko yadda za'a koma kamar da domin yanzu kullum aka bude makarantu akwai yajin aiki ko kuma matsalar albashi. Akwai matsalar wurin karatu da dai makamantansu.
A can baya an sha kafa kwamitoci domin nazari akan ilimi amma kuma ba tare da zantar da shawarwarin da aka tsayar ba dalili ke nan da sakataren kungiyar malaman makaranta Issoufou Arzika ke kira kada taron kwamitin ya zama na "a sha shayi a watse".
Hukumar ilimi ta sha alwashin jan hankalin duk wadanda suke da ruwa da tsaki a harkokin ilimi da su yi aiki da duk abubuwan da kwamitin ya gano.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.