CDS Ta Yi Watsi Da Wa'adin Da Aka Ba Ta

  • Ibrahim Garba

Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Yayin da wa'adin yin babban taron "congre" da Ministan Cikin Gidan Janhuriyar Nijar ya bai wa jam'iyyar CDS ke cika, Shugaban Jam'iyyar Mallam Mahammadu Usumane ya ce Ministan bai da hurumi
Kwana guda kafin cikar wa'adin da Ministan Cikin Gidan Janhuriyar Nijar ya bai wa jam'iyyar CDS Rahama na ta yi babban taron sauya shugabanni wato "congre" ko kuma ta fuskanci rusawa, shugaban jam'iyyar kuma tsohon Shugaban kasa Mahammane Usmane ya ce Ministan bai da ikon ba da wannan umurnin.

Da ya ke jawabi ga taron manema labaran da ya kira yau, Alhaji Mahammane Usmane ya ce abubuwan da su ka shafi wannan jam'iyya na kotu kuma batun wai ta yi "congre" zuwa ran 6 ga watan sha daya ko a rusa ta bai ma taso ba saboda Ministan bai da ikon rusa masu jam'iyya.

Alhaji Mahammane Usumane ya ce tuni ma aka fara tashe tahshen hankula a wasu wurare a kasar bayan kuwa ba a san mutanen kasar sa tashe tashen hankula ba. Ya ce wannan ba wani abu ba ne illa kawai wata kutungwila ta neman gurgunta jam'iyyar CDS. Ya ce sam sam jam'iyyar CDS ba za ta bi umurnin Ministan ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Cikar Wa'adi Ga CDS


.