Daliban da suka fito daga Najeriya a wannan makaranta sun tattauna da wakilinmu Abdoulaye Mamane Ahmadou cikin harshen Faransanchi da suka fara koya, har ma suka bayyana gamsuwarsu da yadda abubuwan suke gudana.
Wata tawaga karkashin jagorancin Kwamishinar Mata da Kyautata Halin rayuwar Al'umma ta jihar Kano, Dr. Binta Jibril, ta ziyarci wannan makaranta domin ganin irin ci gaban da aka samu, da halin da yaran makarantar suke ciki.
Kwamishinar ta ce abubuwan da ta gani, sun kayatar da ita, tana mai fadin cewa wannan makaranta zata kara dankon zumunci a tsakanin Najeriya da Nijar wadanda tun asali ma 'yan'uwan juna ne.
Ta ce ta yi farin cikin ganin yadda daliban makarantar suke zaune cikin farin ciki, suke kuma cudanya da junansu.
Ga rahoton da Abdoulaye Mamane Ahmadou ya aiko daga Nijar.