Bayan 'yan majalisar sun yi kwana uku kan kasafin kudin wakilai 70 suka amince yayin da wasu 43 suka ki amincewa. Daya daga cikin wadanda suka ki amincewa da kasafin kudin Abdu Sala ya ce sun ki amincewa da kasafin domin an dade ana mantawa da wasu batutuwa da suka shafi rayuwar al'umma.Ya ce bara waccan da bara su yaba. Amma a wannan kasafin sun nemi a gyara wajen aikin damina da makarantu da hanyoyi. Ba'ayi ba. To menene zasu gyara.
Nasarar da gwamnati ta samu ta sake nanata karfin da gwamnati ke dashi a majalisar da kujeru 70. Dan majalisa Zakari Umaru ya ce nasarar bata bashi mamaki ba domin makonni biyu da suka shige shugaban gwamnati ya zo wurin majalisa yana neman goyon bayanta. Ya ce kashi 65 na sabon kasasfin kudin za'a a yiwa al'umma aiki manya manya ne.
Ministan kudin kasar Jilbaye ya yi murna ya ce kowace ma'aikata zata yi aiki kain da nain da abun da aka bata.
To saidai fiye da kashi arba'in na kasafin kudin zasu fito ne daga gwamnatocin kasashen waje da masu hannu da shuni.
Abdullahi Maman Ahmadu nada karin bayani,