Babban Bankin Najeriya CBN ya soke lasisin wasu kamfanonin canjin kudi 4,173, cikin kimanin 5000 da ake da su.
ABUJA, NAJERIYA —
Matakin ya biyo bayan sake dawo da tsarin sayarwa kamfanonin dala da tsohon gwamnan bankin Godwin Emefiele ya soke, a mulkin tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Bankin ya ce rashin sabunta kundin lasisi da rashin cika wasu ka'idoji na daga dalilan soke lasisin kamfanonin.
Hakanan bankin ya kafa wata ka'ida ta duk kamfanonin su tabbatar sun tura kimanin kashi 75 cikin 100 na kudin ketare ga abokan huldar su ta hanyar na'ura.
Hakika wadanda aka sokewa lasisin na korafin ba'a yi mu su adalci ba don rashin barin cikar wa'adin daukar matakin.
Kazalika a jerin kamfanonin da aka bari kimanin 700 an ga an maimaita sunan wasu kamfanonin fiye da sau daya.