Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bai Kamata Harkar Canjin Kudade Ta Zama Ta Kowa Da Kowa Ba-Gwamnan Babban Bankin Najeriya


Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Yemi Cardoso
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Yemi Cardoso

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, yace bai kamata a kyale harkar canjin kudade ta zama “ta ci barkatai” ba, inda yace bankin na kokarin fitar da wasu tsauraran ka’idoji domin tsaftace harkar da nufin kawar da ‘yan kayi nayi daga cikinta.

Ya bayyana hakan ne a talatar nan a Abuja a yayin taron fidda manufofin kudi na babban bankin wanda ya gudana a karon farko tun bayan hawansa kan mukamin a watan Satumbar daya gabata.

Najeriya na fama da matsalolin hauhawar farashi da tsadar abinci da faduwar darajar naira da tabarbarewar tattalin arziki da tsadar rayuwa sakamakon janye tallafin man fetur, al’amarin daya haifar da zanga-zanga a wasu sassan kasar.

Darajar Naira ta fadi warwas tun bayan da sabuwar gwamnatin Tinubu ta saketa ba tare da kaidi ba tare da hade harkar canjin kudade a wuri. Takardar kudin ta Najeriya ta tashi daga naira 700 akan dalar Amurka daya a watan mayun bara zuwa fiye da naira 1500 akan dalar a halin da ake ciki yanzu.

Saidai, Cardoso ya bayyana cewar babban bankin na kokarin daukar tsauraran matakai, inda yace CBN zai yi duk me yiyuwa wajen kauda ‘yan kayi nayi daga harkar.

“Muna kokarin samar da tsauraran ka’idoji da zasu tantance waye ya kamata ya gudanar da harkar canjin kudade. abinda muke nufi shine, ba zamu bar ta haka barkatai ba, muna sa ran samu mutanen da zasu yi da gaske da nufin hidimtawa al’umma ba wai kawunansu ba.”

Cardoso ya kara da cewar za’a yi amfani da fasahar zamani a harkar canjin kudaden kuma ka’idojin zasu kara zaburar da gogayyar kasuwanci da zata ragewa ‘yan Najeriya farashin dala tare da sama musu dimbin alfanu.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG