A cewar jaridar, babban daraktan bincike na bankin CBN, Ganiyu Amao yayi jawabi a ranar Litinin a wani taron da kwamitin majalisar wakilai ya shirya domin bincikar yanayin matatun man fetur na kasa, inda ya bayyana cewa, adadin ya kasance daga cikin dala biliyan 119.4 da aka kashe kan shigo da kaya a wannan lokacin.
Amos yace yawaitar fitar kudade daga kasar na shafan kokarin da bankin ke yi na saka ido a hadadar kudade.A cewarsa, wannan na shafan ajiyar da kasar keyi a kasashen waje wanda hakan na shafar darajar kudin Naira.
Ya kara da cewa, "Bayanai daga CBN na nuni da cewa, daga shekarar 2013 zuwa 2017 yawan musayar kudaden kasashen waje da aka fitar don sayayya a kasashen waje ya tsaya a dala biliyan 119.41, yayin da musayar kudaden da aka fitar don shigo da man fetur ya tsaya a dala biliyan 36.37.
Shugaban gudanar da aikace-aikace na ma’aikatar man fetur ta kasa NNPC Anibor Kragha, ya bayyana cewa abin da ya fi muhimmanci yanzu shine, kasar ta duba matatun man fetur din da ta ke da su ta kuma a gyarasu domin samun sauki kan biliyoyin kudaden da ake kashewa ta hanyar fita da shiga dashi.