Shugaba Buhari ya amince da kafa sabuwar bataliyar rundunar Sojin Najeriya, da sabon ofishin ‘yan sanda a karamar hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna a wani yunkurin tsaurara matakan tsaro a yankin, biyo bayan hare-haren ‘yan bindiga.
A wata sanarwar da Gwamnatin Najeriya ta fitar da sa hannun kakakinta,Garba Shehu, Shugaba Buhari ya yi amfani da babban murya wajen yin Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa jama’ar da ba su ji ba su gani ba a kauyen Gwaska.
“Ina jin zafin tashin hankalin da iyalan wadanda suka rasa rayukansu suke fuskanta kuma wannan gwamnatin za ta yi iya kokarinta wajen ganin an sami galaba kan wadannan makiyan bil adama.”
A ranar litinin 7 ga watan Mayu, Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-Rufai ya je ziyarar jaje a Birnin Gwari inda ya gana da Sarkin garin, Mallam Jibril Zubair II da sauran shugabannin al’ummar garin kafin ya wuce zuwa kauyen Gwaska.
“Ina son ku sani cewa abun na ranmu kuma da yardar Allah zamu yi bakin kokarinmu wajen magance wannan tashin hankali na rashin imani.” Inji El-Rufai.
A ranar Asabar ne wadansu ‘yan bindiga suka yi wa mutanen kauyen Gwaska a karamar hukumar Birnin Gwari kisan gilla. Kawo yanzu adadin wadanda suka rasa rayukansu ya kai hamsin da takwas a cewar Sarki Jibril Zubair II.
Saurari rohoton Isa Lawal Ikara
Facebook Forum