Jawabin babban malamin na addinin Kirista Rev. Matthew Hassan Kukah wanda ya gabatar ranar 13 ga wannan watan na Yuli ya nuna yadda gwamnati ke nuna halin ko in kula kan yadda 'yan-bindiga ke afkawa Kiristoci.
Sai dai gwamnatin tarayya ta ce san rai da siyasa ne cike da jawabin babban malamin saboda haka ba dalilin kula shi.
Wannan sa-in-sa dai ta sa kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN), reshen jihar Kaduna fitowa don marawa Rev. Matthew Hassan Kukah baya ta na me cewa duk abubuwan da ya fada haka yake.
Daya daga cikin masu fashin baki kan harkokin tsaro wanda ya saba nuna gazawar gwamnatin tarayya, Manjo Yahaya Shinko mai ritaya ya ce matsalar tsaro a Najeriya dai ta shafi kowa ne kuma bai kamata ana saka addini a ciki ba.
Karin bayani akan: Kiristoci, Musulmai, Muryar Amurka, Rev. Matthew Hassan Kukah, Kiristoci ta Kasa, Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, jihar Kaduna, Nigeria, da Najeriya.
"Duk wanda ya san yadda 'yan bindigar nan suke gudanar da ayyukansu, in muka duba za mu ga tamkar wadanda suka fi samun matsala, bangare ne na Musulmi, misali, ana maganar arena maso gabas, arewa ta tsakiya da area ta yamma, duk irin wuraren da ya ambato yake cewa an takura su, za ka duba ka ga bai kai fadin irin wadannan wurare da na ambata ba." In ji Shinko.
Martanin da gwamnatin tarayya ta mayawar Rev. Matthew Hassan Kukah dai ya sa shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN a Jihar Kaduna, Rev. John Joseph Hayeph ya ce ya kamata gwamnati ta gane gyara kayanka dai bai taba zama sauke mu raba ba.
"In za a fadi gaskiya, abin da Bishop Kukah ya fada, abu ne da dukkanmu Kirista da ma wadanda ba Kirista ba, mun san yana faruwa, mun san yadda ake mana danniya."
A farkon makon nan Bishop Kukah ya bayyana a gaban majalisar dokokin Amurka ta yanar gizo inda rahotanni suka ce ya ce ana muzgunwa mabiya addinin Kirista a Najeriya karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Kukah ya kuma yi ikrarin cewa hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa, ya fi karkata akan Kiristoci, zargin da gwamnatin ta musanta.
“Tare da nuna girmama matsayar da malamin addinin ya dauka, bayanan da suke a bayyane karara, sun nuna cewa ikirarin da ya yi cewa ‘yan bindiga ko ‘yan ta’adda na kaikaitar makaranta Kiristoci ba daidai ba ne.” In ji kakakin Buhari Malam Garba Shehu.
Maganar matsalar tsaro da hare-haren 'yan-bindiga a jihar Kaduna dai na kara ta'azzara domin ko a makon jiya sai da gwamnatin ta ce 'yan-bindiga sun kashe mutum 222, sannan su ka sace 774 cikin watanni ukun da su ka wuce a fadin jihar baki daya.
Saurari rahoto cikin sauti daga Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5