Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadar Shugaban Najeriya Ta Soki Sharuddan Da Aka Gindayawa Rev. Kukah


Rev. Matthew Hassan Kukah, hagu da Shugaba Buhari a dama, Gen. Abdulsalam, tsakiya (Twitter: Fadar gwamnatin Najeriya)
Rev. Matthew Hassan Kukah, hagu da Shugaba Buhari a dama, Gen. Abdulsalam, tsakiya (Twitter: Fadar gwamnatin Najeriya)

Gwamnatin Najeriya ta ce ya zama dole a bar Rev. Matthew Hassan Kukah ya yi addininsa da siyasarsa ba tare da tsangwama ba.

Fadar shugaban Najeriya ta ce kuskure ne da kungiyar hadin kan Musulmi ta “Muslim Solidarity Forum” da ke Sokoto ta gindayawa Rev. Matthew Hassan Kukah wasu sharudda kan kalaman da ake zargi ya yi na “batanci” akan Musulunci.

A ranar Talata kungiyar ta bayyana a wani taro da ta gudanar a Sokoto cewa, Rev. Kukah ya fito ya ba al’umar Musulmi hakuri kan kalaman da ya yi ko kuma ya fice daga jihar ta Sokoto.

Sai dai wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar sanye da sa hannu mai bai wa shugaba Buhari shawara kan sha’annin yada labarai Malam Garba Shehu da yammacin Laraba, ta nuna cewa “hakan kuskure ne, saboda ya sabawa kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.”

“Karkashin kundin tsarin mulki, kowane dan kasa yana da ‘yancin fadin albarkacin bakinsa, ya mallaki kadara, ya zauna a duk yankin da ya ga dama, ya kuma wataya ba tare da an muzguna ma shi ba.” Sanarwar ta Garba Shehu ta ce.

“Karfin Najeriya ya rataya ne akan al’umomi daban da take da su. ‘Yancin addinai su yi cudanya da juna na nan kunshe a kundin tsarin mulki. Hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnati, musamman ma wannan ta dimokradiyya, ta tabbata ana girmama kundin tsarin mulkin. Amma kuma ya zama dole, kowa ya rika mutunta dan uwansa dan Najeriya tare da gujewa abin da zai bata rai.” In ji fadar shugaban kasa.

“Father Kukah ya matukar batawa mutane da dama rai da kalamansa masu cike da takaddama akan gwamnati da shugaban kasa, inda har wasu suke zarginsa da laifin furta kalaman nuna kiyayya ga addinin Musulunci.”

“Karkashin dokokimu, dole ne kungiyoyi ko rassa su gujewa ba da wa’adin ficewa daga wani yanki, sannan kada su dauki doka a hannu kan wani abu da suke ganin ba’a yi daidai ba. Kotu ce kadai take da wannan hurumi. Yin gaban kai ba shi ne mafita ba.”

Ko bayan kalaman da Bishop Kukah ya yi a sakon Kirsimati wanda ya tabo batutuwa da dama, a wata ganawa da manema labarai bayan Kirsimatin, ya nanata cewa shi kalamansa ya yi su ne bisa fahimtarsa ba dole ne sai an yarda da su ba.

Ya kara da cewa ya fadi abin da ke cikin ransa ne ba wai don ya fi kowa ilimi ko sanin abin da kan kai ya koma ba ne, sai dai don ya samu damar fitar da abin da ke ransa ne kuma ba dole ne mutane su yarda da abin da ya fada ba ko kuma cewa lalle daidai ne ya fada ba, duk dan Adam yana da damar magana kuma ba lallai ne abin da ya fada ya zamo daidai ba ko kuskure.

Karin bayani akan: Matthew Hassan Kukah, Sokoto​, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG