Wannan tabbacin ya fito ne daga ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya wanda ya nuna damuwa akan halin da ‘yan kasar suke ciki na rashin tsaro.
Matsalar rashin tsaro a Najeriya sai kara ta'azzara take yi domin yanzu ba yankin arewa kadai ba har kudu babu mai tabbas ga rayuwar sa.
A yankin arewa maso yammacin kasar kullum jama'a cikin zullumi suke domin kowane lokaci suna iya fuskantar hare haren ‘yan bindiga inda akasari akan samu salwantar rayuka da kuma wawure dukiyoyi.
Yanzu haka mutanen yankin Sakaba a yankin Zuru ta jihar Kebbi suna cikin wannan hali na rashin tabbas tamkar yadda wasu mazauna yankin suka fada.
Karin bayani akan: Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, Burtaniya, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Bisa ga damuwa da halin da jama'a suka tsinci kansu ciki kasar Burtaniya ta ayyana shirin ta na taimakawa yankin arewa dake fama da matsalar acewar jagoran wani ayari daga ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya Samuel Waldock.
“Da yake kuna fadi tashi da matsalar rashin tsaro a arewa Maso yamma mu kasar Burtaniya mun lura da halin da Sakkwato da sauran jihohin arewa Maso yamma suke ciki saboda wadannan kalubale da kuma halin kunci da suka saka jama'a, da yake kuna fama da wannan matsalar zamu taimaka muku fita daga wannan babbar matsala"
A hirar shi da Muryar Amurka, gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal wanda shine mataimakin shugaban dandalin gwamnoin Najeriya yace kasar Burtaniya ita ce tafi cancanta ta taimakawa Najeriya ta samu fita daga wannan yanayin musamman duba da tarihin kasashen biyu.
“Hakika wannan abin damuwa ne yanayin da muke ciki kuma muna neman dauki kuma ba wadanda ya fi dacewa su taimaki Najeriya a wannan halin kunci kamar kasar Burtaniya.”
Bisa ga cewar gwamna Tambuwal, girman matsalolin rashin tsaro a Najeriya, kasashen da suka ci gaba a duniya kamar kasar Amurka da Burtaniya ke ta ayyana shirin su na taimakawa wajen shawo kan matsalolin.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5