Prime Ministan kasar Somalia, Hassan Ali Khaire, ya umurci ‘yan sanda da jami'an leken asiri da su gaggauta inganta matakan tsaro a Mogadishu, babban birnin kasar, a bayan wani harin da kungiyar Al’shabab ta kai wanda yayi sanadin mutuwar mutane kusan 40 a ranar jumma'ar data gabata.
Harin na ranar jumma'a shine irinsa na farko da kungiyar ta Al’shabab ta kai a babban birnin kasar tun cikin watan oktoban bara inda wata babbar mota ta tada bam da yayi dalilin mutuwar mutane sama da 500, sai kuma wani harin da suka kai a hotel sati daya bayan aukuwar na babbar mota, nan ma mutane 30 suka mutu.
‘’Tsaro shine babban abinda muka sa gaba yanzu’’Inji Khaire, Ba zamu yarda da kashe mutanenmu ba, ba zamu yi kasa a gwiwa ba, don harin tada bam guda ko biyu, wajibi ne ku tabbatar da an kawo karshen rashin tsaro a Magadishu.
Facebook Forum