Burkina Faso, Mali Da Nijar Sun Kai Ukraine Kara A Majalisar Dinkin Duniya

NIGER-BURKINA FASO-MALI

Hukumomin mulkin sojan Burkina Faso, Mali da Nijar sun rubutawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wasika domin yin Allah-wadai da zargin goyon bayan da kasar Ukraine ke yi wa kungiyoyin 'yan tawaye a yankin Sahel da ke yammacin Afirka, kamar yadda kwafin wasikarsu ta nuna.

Mali ta yanke huldar diflomasiyya da Ukraine a farkon wannan wata saboda kalaman da mai magana da yawun hukumar leken asirin sojin Ukraine ya yi game da fada a arewacin Mali wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojojin Mali da sojojin hayan Wagner na Rasha a karshen watan Yuli.

NIGER-BURKINA FASO-MALI

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta bi sahun kwanaki bayan nan ta nuna goyon baya ga makwabciyarta.

Takaddamar dai ta barke ne bayan da kakakin hukumar leken asirin sojin Ukraine ya ce 'yan tawayen Mali sun samu bayanan da ake bukata domin kai harin na watan Yuli.

Ibrahim Traore da Abdourahamane Tiani

Mali da Nijar sun zargi Ukraine da goyon bayan "ta'addancin kasa da kasa".

Ukraine dai ta sha kiran wannan zargi mara tushe da kuma cewa ba gaskiya ba ne. Ita ma wata ‘yar kawancen 'yan tawayen Abzinawa ta ce ba ta samun wani tallafi daga Ukraine ba.

-Reuters

Saurari karin bayani daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Burkina Faso, Mali Da Nijar Sun Kai Ukraine Kara A Majalisar Dinkin Duniya