WASHINGTON D.C —
A shirinmu na nishadi, yau muna tare da Fiddausi Sheka, matashiyar mawakiya da ta fara waka shekaru hudu da suka gabata kuma kamar yadda matashiyar ta bayyana, akwai wakoki da dama masu ma'ana kuma masu jan hanali da ta rera wadanda suka sa tayi fice.
Fiddausi ta kara da cewa a cikin wakokin ta, wadanda tasa ma suna sharrin zuciya, da marainiya na daga cikin wakokin da suka yi suna kwarai kuma sun sami karbuwa ga jama'a.
Burin Fiddausi dai shine, sakon da take aika ma al'uma ta hanyar waka ta kai ga kunnuwan jama'a domin su yi aik da irin shawar wari da fadakarwar da take aikewa wadanda a cewar ta tamkar wa'azi ne ta wani bangaren.
Ga cikakkiyar hirar..