Gwamnatin da ta shude ta dauki malamai dari hudu da talatin da suka yi watanni bakwai suna aiki amma ba'a biyasu ko kwandala ba.
A karkashin gwamnatin Barrister M.A. Abubakar ta biya malaman hakkinsu na watanni bakwan da ba'a biya ba. Ta biyasu kudi kusan nera miliyan dari.
Gwamnatin yanzu ta gaji bashi na fiye da nera miliyan dari biyu akan ciyar da dalibai. Yanzu kowane wata gwamnati tana rage bashin da nera miliyan tamanin domin taga an warware matsalolin ilimi.
Dangane da kudaden da aka sha warewa domin ilimi amma kuma ba'a yi anfani dashi kan ilimin ba Sabo Muhammad yace idan ba'a kawar da cin hanci da rashawa ba tabbas zai kashe Najeriya. Dalili ke nan da gwamnatin jihar tana binciken takardun malamai da wadanda basu da alaka da ilimi amma aka basu aikin koyaswa.
Shi ma Malam Aminu Sidi mai fafutikar kare ilimi yace ba za'a iya kwatanta arewa da kudu ba akan harkokin ilimi domin mutanen kudancin Najeriya sun tserewa arewa akan ilimi. Yace abu na biyu kuma da ya nakasa ilimi a arewa shi ne ta'adancin 'yan Boko Haram wanda ya sa masu sha'awar ilimi na guje masa. Abu na uku yace wadanda suka kware a karatun basu cika shiga harkokin koyaswa ba.
Soke makarantun horas da malaman makarantu ya yiwa arewa illa musamman jihar Bauchi. Siyasa kuma ta shiga harakar ilimi. Misali yawancin malaman cikin birni matan manyan mutane ne ko danginsu wadanda basu kware ba sai dai su je makarantu su shimfida tabarmi su yi kwanci ko kuma su baza kayan da suke sayarwa.
Ga karin bayani.