Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar-Najeriya Ta Kafa Tarihi, Manyan Jami'o'in Duniya 8 Sun Bata Gurbin Karatu


Hakika idan ana maganar mutane masu hazaka a fadin duniya, babu shakka sai anyi maganar ‘Yan-Najeriya. A duk kasar duniya da akayi maganar wani cigaba to sai kaga ‘Dan ko ‘Yar Najeriya a cikin jerin masu bada gudunmawa a duniya gaba daya.

Augusta Uwamanzu-Nna, ‘yar makarantar sakandire ce, a garin Long Island, na jihar New York, a kasar Amurka. Kuma ‘yar asalin Najeriya ce, duk dai da cewar an haifeta a kasar Amurka, amma a duk lokacin hutu iyayen ta kan kaita Najeriya. Wanda hakan ya kara sa mata kwarin gwiwar karatu, ganin yadda take ganin ‘yan uwanta suke a gida Najeriya, basu da damar da take da na karatu a kasar Amurka.

Yanzu haka dai wanna yarinyar ta bar tarihi, inda ta gama makarantar sakandire da maki GPA101.6 wannan wani abun yabawa ne domin kuwa ba kowane yaro ne ke iya samun wannan makin ba. Hakan yasa manya-manyan jami’o’I a duniya da sukayi fice guda takwas suka bata gurbin karo karatu wato (Admission). Jami’o’in dai su hada da Brown University, Columbia University, Cornell University, Dartmouth College, Harvard University, Princeton University, da University of Pennsylvania haka da Yale University. Sauran sun hada da Johns Hopkins University, Massachusetts Institute of Technology, New York University da Rensselaer Polytechnic Institute.

A cikin jawabin ta, tace lallai idan matasan Najeriya suka tashi tsaye wajen karatu duk dai da cewar basu da irin abubuwan da suke da su a nan kasar Amurka, zasu iya cinma burin su. Tace har ya zuwa yanzu bata tsayar da shawarar wace makaranta zataje ba cikin su, amma tana sa ran idan tayi shawara da iyayen ta zata dauki daya daga cikin takwas din.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG